30 Yuni 2020 - 09:18
Tarayyar Turai Ta Tsawaita Takunkuman Da Ta Dorawa Kasar Rasha

Kungiyar tarayyar Turai (EU) ta bada sanarwan tsawaita takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar Rasha na wasu watannin 6 masu zuwa.

(ABNA24.com)  Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya nakalto bayanin bayan taro wanda wakilan kasashen kungiyar suka fitar a jiya litinin a birnin Brussels, yana cewa, an tsawaita takunkuman har zuwa watan Jenerun shekara ta 2021.

Labarin ya kara da cewa tun lokacin da kungiyar ta zargi kasar Rasha ta tallafawa yan a waren kasar Yukrain a shekara ta 2014 ne ta dorawa kasar ta Rasha wasu takunkuman tattalin arziki.

Har’ila yau ballewar yankin Creamier na kasar Yukrain da kuma hada shi da kasar Rasha na daga cikin matsalolin da turawan su ke takaddama da kasashen na Turai.



/129